Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Benuwai ta tabbatar da mutuwar fasinjoji 20 a wani hatsarin jirgin ruwa da ya faru a Kogin Benuwai ranar Asabar da ta gabata.
Kakakin rundunar, Catherine Anene, ta ce an ceto mutane 11 daga kogin, yayin da aka gano gawarwaki 20, kuma ana ci gaba da gudanar da aikin ceto domin nemo sauran wadanda suka bace.
A cikin wata gajeriyar sanarwa, ta ce, “Mun tabbatar da faruwar hatsarin jirgin ruwa, kuma ana ci gaba da aikin ceto. Mutane 11 sun tsira, yayin da aka gano gawarwaki 20.”
Rahotanni sun nuna cewa wadanda hatsarin ya rutsa da su suna kan hanyarsu ta komawa Apochi da Odenyi a karamar hukumar Doma ta Jihar Nasarawa, bayan sun bar kasuwar Ocholonya da ke karamar hukumar Agatu ta Jihar Benuwai, lokacin da jirgin ruwan katakinsu ya kife.
Wani mazaunin garin Ocholonya mai suna Adanyi, ya shaida wa manema labarai cewa jirgin ruwan na dauke da fiye da mutane 20, yawancinsu mata da yara, lokacin da hatsarin ya faru.