Asalin hoton, AFP
Akwai yara da jami’ai a lokacin da aka kai harin na kunar-bakin-wake a wurin
Jami’ai a Jamhuriyar Dumokuradiyyar Kongo sun ce mutane akalla shida ne suka mutu a wani harin kunar-bakin-wake da aka kai wani wurin cin abinci da yake makare da jama’a a birnin Beni da ke gabashin kasar.
‘Yan sanda sun dakatar tare da hana dan kunar-bakin-waken shiga ginin, amma sai ya tayar da bam din da ke jikinsa a kofar inda ya kashe kansa da wasu mutane biyar, da wasu goma sha uku da suka samu raunuka.
Duk da cewa babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin, hukumomi na zargin kungiyar Allied Democratic Forces (ADF), mai alaka da kungiyar Islamic State (IS) da ke ikirarin jihadi.
Mutane sama da 30 ne suka taru wurin cin abincin inda suke bikin Kirsimeti lokacin da bam din ya tashi kamar yadda wasu da abin ya faru a gabansu suka sheda wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Rahotanni sun ce akwai yara da jami’ai a wurin lokacin da aka kai harin, kuma ya rutsa da wasunsu.
Wani mai gabatarwa a wata tashar rediyo, ya yi wa AFP bayani, inda ya ce, ”ina zaune a nan. Akwai wani babur da ke ajiye a nan. Sai kawai na ji babur din ya tafi bayan da aka ji wata kara mai karfin gaske.”
Bayan fashewar jami’in sojan da ke kula da dokar-ta-bacin da aka kafa a yankin gabashin kasar ta Jamhuriyar Dumokuradiyyar Kongo ya gaya wa jama’a da su koma gidajensu domin tsaron lafiyarsu.
A ‘yan makwannin nan ana samun dauki-ba-dadi tsakanin sojoji da masu ikirarin jihadi a Beni.
A watan Nuwamba dakarun Kongo da na Uganda suka fara wani aikin tsaro na hadin gwuiwa domin kawo karshen miyagun hare-haren kungiyar ta ADF.
Hukumomi a Uganda sun ce kungiyar ce take da alhakin kai wasu jerin hare-hare a kasar a kwanan nan, ciki har da wani da aka kai babban birnin kasar Kampala.
A shekarun 1990 ne wasu da ba sa jin dadin yadda gwamnati ke yi wa Musulmi suka kafa kungiyar mai gwagwarmaya.
Sai dai kusan an kore ta daga yammacin Uganda, amma sauran mayakanta suka tsere zuwa kan iyaka da Jamhuriyar Dumokuradiyyar Kongo.
Daga nan ta kafa kanta a gabashin Kongon, kuma ana zarginta da kisan dubban farar hula a can a cikin shekara goma da ta wuce, ciki har da hare-hare a kan Kiristoci.
A watan Maris Amurka ta sanya sunan kungiyar cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke da alaka da IS.
Ita ma kungiyar ta IS ta fito fili ta ce ADF din tana da alaka da ita.