Hanyar Kaduna-Abuja: Tsaron hanyar ya gagari hukumomi ne?

Buhari

Tare hanyar Abuja zuwa Kaduna da wsu ‘yan bindiga masu satar mutane suka yi a ƙarshen mako inda suka sace mutane da dama sannan suka kashe wasu, ta sake tayar da hankalin jama’a musamman waɗanda ke yawan bin hanyar.

Ganau sun ce ‘yan bindigar sun tare hanyar ce da yammacin ranar Lahadi, inda suka kwashe tsawon lokaci suna harbe-harbe lamarin, da ya yi sanadin mutuwar mutum fiye da da 15.

Kazalika, ‘yan bindigar sun sace mutane da dama wadanda har yanzu ba a kai ga sanin adadinsu ba.

Sai dai a sanarwar da gwamnatin jihar Kaduna ta fitar ta ce mutum biyu ne suka mutu sakamakon harbe-harben da ‘yan bindigar suka yi, tana mai cewa jami’an tsaro sun ceto mutum tara daga cikin wadanda aka sace.

Yadda lamarin ya faru

Bayanan hoto,
A wasu lokutan akan samu mummunan cunkoso a hanyar duk da fama da rashin tsaro

Waɗanda suka shaida lamarin sun faɗa wa BBC cewa da yammacin ranar Lahadi ne ‘yan bindigar suka bude wuta kan motocin matafiya, inda suka kashe mutane da dama sannan suka sace wasu.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindigar sun kashe kimanin mutum 15, kodayake hukumomi sun ce mutum biyu aka kashe.

Wata sanarwa da Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Kaduna Samuel Aruwan ya fitar da yammacin Lahadi ta ce dakarun tsaro da ke sintiri sun ceto mutum tara daga cikin wadanda da aka sace.

“Masu dauke da bindigogi sun bude wuta kan wata motar bas, inda suka tilasta wa direba tsayawa. A yayin da [jami’an tsaro] suka isa wurin, tuni ‘yan bindigar suka sace mutum tara daga bas din mai daukar mutum 18…

“Nan da nan dakarun suka soma fafatawa da ‘yan bindigar kuma hakan ne ya sa suka tseratar da mutum tara da aka sace…sai dai abin takaici direba da mutumin da ke zaune kusa da shi sun mutu,” in ji Mista Aruwan.

Martanin masu amfani da shafukan sada zumunta

Da yawa cikin masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi ta rawaito lamarin lokacin da yake faruwa, tare da tura hotuna da bidiyon abin da ke faruwa kai-tsaye a kan titin.

Wannan mai shafin amfani da Twitter cewa ya yi, “Bayar da lokacinka kaɗan ka kalli wannan bidiyon kan abin da ke faruwa a kan babbar hanyar Abuja-Kaduna,” ya kuma tambayi shugaban ƙasa cewa “mai muka yi muke fuskantar wannan abu? a taimaka a kawo karshen rashin tsaro”.

Safyanu ya ce: “Tunasarwa ce, a 2017 titin Abuja-Kaduna kalau yake, lokacin da aka mayar da jiragen da za su sauka a Abuja su riƙa sauka a Kaduna, an samar da cikakken tsaro saboda rayukan mutanen da za su bi titunan sun cancanci a kare su”.

Shi kuwa Modibbo Sunusi cewa ya yi: “‘Yan bindiga sun kai hari jami’ar ABU, sun kai hari kwalejin Nuhu Bamalli, sun kashe mace mai ciki, ‘yan bindiga a babbar hanyar Abuja-Kaduna amma gwamnanmu El-Rufa’i ya gaza cewa komai. Ina gwamnanmu? Kisan ya yi yawa, shirun ya yi yawa, ya kamata mu dauki mataki yanzu.”

Waiwaye

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da lamuran tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a yankin arewacin Najeriya, musamman a jihohi irinsu Kaduna da Zamfara da Katsina.

Ko a karshen makon nan, sai da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka shiga kwalejin Nuhu Bamalli da ke wajen birnin Zariya, inda suka sace wani malami suka kuma harbi mutum ɗaya a hannu tare da sace ‘ya’yansa biyu.

Rahotanni sun ce mutumin da aka harba yana asibiti yana jinya, a gefe guda kuma, yana cikin damuwar ‘ya’yansa da aka yi awon gaba da su.

A garin Jangebe da ke Talatar Mafara a jihar Zamfara, al’ummar yankin sun ce sun kwana cikin juyayi na mutanensu sama da 30 da aka sace a kan hanyarsu ta komawa kauyukansu daga kasuwar Bagega a yammacin ranar Asabar.

Wani da ya tsira daga harin ‘yan fashin ya ce, ‘yan fashin sun harbi akalla mutum ɗaya cikin wadanda suka tare.

A mafi yawan lokuta idan aka tuntuɓi hukumomi game da ta’azzarar wannan lamari sai su ce suna iya bakin ƙoƙarinsu wajen daƙile wannan al’amari.

More from this stream

Recomended