
Ana sa Ran cewa Mahukuntan kasar ta Saudiyya zasuyi Karin Bayani ga Duniya a cikin Satin nan akan yiyuwa ko akasin hakan akan Aikin Hajjin n bana #Hajj1441 kamar yadda Jaridar @FinancialTimes ta Bayyana.
Wadannan Jerin Kasashen dai su sun bayyana soke zuwan Mutanen Kasashen nasu Hajjin Bana a Wannan Shekarar, Kasashen sun hada da:
1. Indonesia
2. Brunei
3. South Africa
4. India (An Bayyana cewa harma ta Maida ma Maniyyata Kudaden su)
5. Malaysia
6. France
7. Singapore
8. Australia and New Zealand
Allah ya Tabbatar Mana da Alkhairi Amin, duk wannan yana faruwa ne sanadiyyar Annobar Chutar Korona Bairos da ta Addabi Duniya Baki Daya.