Hakeem Baba-Ahmed Ya Shawarci Shugaba Tinubu Da Kada Ya Sake Fitowa Takara a 2027

Tsohon mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin siyasa a ofishin mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, Hakeem Baba-Ahmed, ya shawarci shugaban ƙasar da kada ya sake neman tazarce a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

A wata hira da ya yi a shirin Politics Today na tashar Channels Television, Baba-Ahmed ya ce maimakon hakan, Tinubu ya mai da hankali wajen gyara Najeriya da kuma shirya matashi wanda zai gaje shi.

Ya ce: “Da na samu ganawa da Shugaba Tinubu, da na ce masa kada ya tsaya takara a 2027, ya tallafa wa wani matashi.”

Baba-Ahmed ya ƙara da cewa akwai abubuwa da dama da shugaban na iya yi cikin shekaru biyu da suka rage masa fiye da sake neman shugabanci, ciki har da gyaran abin da bai samu damar yi ba da kuma ciyar da ƙasar gaba.

“Akwai ‘yan Najeriya da dama masu kishin ƙasa kuma masu sha’awar bada gudummawa, ya kamata a ba su dama su gwada shugabanci. Tinubu ya yi nashi, ya bar sauran,” a cewar Baba-Ahmed.

Baba-Ahmed ya kammala da roƙon Shugaban ƙasa da ya mai da hankali kan gyaran tattalin arziki da harkokin tsaro a cikin lokacin da ya rage masa kafin wa’adin mulkinsa ya ƙare.

More from this stream

Recomended