
Asalin hoton, AFP
Musulmi sun soma aikin Hajjin bana a kasar Saudiyya, ko da yake a wannan shekarar mutanen da ke aikin na Hajji ba su da yawa saboda annobar korona.
Mahajjata 10,000 ne ake sa ran za su gudanar da aikin Hajjin bana sabanin mutum miliyan biyu da suka gudanar da aikin bara.
Galibin mutanen da suke zuwa aikin Hajji ‘yan kasshen waje ne, amma wannan shekarar za a bar ‘yan kasashen wajen da ke zaune a Saudiyya ne kawai su yi Hajji.
An gwada zafin jikin mahajjatan bana sannan aka yi musu gwajin cutar korona a yayin da suka isa birnin Makkah a karshen makon jiya, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.
Kazalika za a killace mahajjata kafin su soma aikin Hajji sannan a sake yi musu gwaji bayan kammala aikin na Hajji. Haka kuma dole ne mahajjata su sanya takunkumin rufe fuska.
A hirarsa da gidan talbijin na al-Arabiya a farkon mako, Ministan Aikin Hajji Mohammed Saleh Binten ya ce an killace mahajjata a gidajensu kafin a sake killace su na kwana hudu a otal-otal da za su sauka a Makkah.
Saudiyya ta bayar da rahoton mutum 270,000 da suka kamu da cutar korona sannan cutar ta yi ajalin kusan mutum 3,000,inda ta zama daya daga cikin kasashen da suka fi fama da cutar a Gabas Ta Tsakiya.
Yin aikin Hajji na cikin Shika-shikan Musulunci guda Biyar – kuma ana so duk mutumin da ke da hali da kuma lafiya ya gudanar da aikin Hajji akalla sau daya a rayuwarsa.
Mahajjata suna taruwa a Makkah domin tsaiwar Arafat, wadda daya ce daga cikin shika-shikan aikin Hajji.