Haɗarin tankar mai ya yi ajalin mutane kusan 30 a Neja

Fashewar wata tankar mai ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 30 a hanyar Agaie-Bida a jihar Neja da safiyar Lahadi

Rahotanni sun tattaro cewa tankar ta yi karo ne da wata tirela da ke dauke da shanu kuma ta nufi jihar Legas daga Wudil, jihar Kano.

Babban daraktan hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja, Mallam Arah, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Zuwa yanzu dai ba a samu rahoton abin da hukumar kiyaye haɗɗura a Najeriya (FRSC) ta ce kan hadarin ba.

More from this stream

Recomended