Mutane 14 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 13 suka samu raunuka daban-daban a wani hatsarin da ya faru a unguwar Aloma da ke karamar hukumar Ofu a jihar Kogi.
Hatsarin da ya afku a ranar Lahadin da ta gabata ya hada da wata motar bas kirar Toyota Sienna da ta nufi Abuja daga Fatakwal da wata motar bas kirar Toyota Hiace da ta nufi Kudancin kasar.
Shaidun gani da ido sun ce hatsarin ya afku ne a lokacin da wasu motocin kirar Toyota guda biyu na kasuwanci suka yi karo da juna.
Wani ganau ya ce, “Mutane 13 da suka hada da direban Hiace Bus gaba daya gobarar ta kone.
Amma daya daga cikin mutane hudu da suka tsira a cikin motar bas din sun mutu a asibiti saboda konewar da suka samu wanda ya kawo adadin zuwa 14 da suka mutu.