A yanzu dai za a iya cewa gwamnan jihar Rivers,Nyesom Wike ya zama turare dan goma ganin yadda kowane bangare na manyan Jam’iyun APC da PDP ke neman ya kasance tare da su.
A yayin da jam’iyar PDP ke kokarin yin duk me yiyuwa domin ganin Wike bai sauya sheka ba ita kuwa jam’iyar APC zawarcin gwamnan take domin ya dawo cikinta.
Koda a ranar Juma’a sai da wasu gwamnonin jam’iyyar uku suka kai masa ziyara.
Gwamnonin sun hada da,Kayode Fayemi na Ekiti,Babajide Sanyaolu na jihar Lagos da kuma Rotimi Akeredolu na jihar Lagos.

