Gwamnoni ne matsalar Najeriya – Ghali Umar Na’Abba

Latsa hoton sama domin kallon bidiyon

Tsohon kakakin majalisar wakilai ta Najeriya Hon Ghali Umar Na’Abba ya zargi gwamnoni da cewa su ne matsalar Najeriya da ke kassara dimokaradiyya a ƙasar.

A hirarsa da BBC ya ce gwamnoni suka haddasa duk wani halin da yanzu Najeriya ta tsinci kanta a ciki.

Duk ana ganin dimokaradiyya a Najeriya wuyanta ya isa yanka, amma tsohon shugaban majalisar wakilan Najeriya na ganin da sauran aiki idan aka yi la’akari da manyan matsalolin da suka dabaibaye dimokuradiyyar Najeriya, a cewarsa saboda rashin dimokaradiyyar cikin jam’iyya da siyasar uban gida da kuma siyasar ɓangaranci.

Na’Abba wanda aka zaɓa ɗan majalisar tarayya a jam’iyyar PDP kafin ya koma APC, ya ce yanzu dukkanin manyan jam’iyyun babu wadda take bin tsarin dimokuradiyya.

“Yanzu ba ni da jam’iyya saboda ba dimokuradiyya ake ba, kuma ba a yin zaɓe.”

“Na janye daga takarar sanata saboda an bukaci dole sai na bayar da kudi a tsayar da ni,” in ji shi.

Ya shaida wa BBC cewa suna shirin kafa sabuwar jam’iyyarsu kuma zai nemi takarar kujerar sanata.

More from this stream

Recomended