Gwamnatin Zamfara ta ba wa ma’aikatanta romon karshen shekara

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da biyan albashin watan 13 ga dukkan ma’aikatan gwamnati a jihar.

Gwamnati ta sanar da hakan ne a ranar Alhamis a wata sanarwa da shugaban ma’aikata, Ahmed Liman ya fitar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Idris, ta bayyana hakan a matsayin babban lamari wanda ya yi daidai da kudurin gwamnati na jin dadin ma’aikata da kuma kara zaburar da ma’aikata.

Sanarwar ta kara da cewa, “A yau, Gwamna Dauda Lawal ya amince da biyan kudaden lamuni na karshen shekara ga jama’a da ma’aikatan gwamnati a jihar Zamfara.

“Ya kamata a lura cewa wannan shi ne karo na farko a tarihin Zamfara da gwamnatin jihar ke biyan ma’aikata albashin watan 13.”

More from this stream

Recomended