Gwamnatin Kano Za Ta Biya Biliyan 3 Ga Mutanen Da Aka Rusawa Shaguna A Filin Idi

Gwamnatin jihar Kano ta amince ta biya naira biliyan 3 a matsayin diya ga mutanen da aka rusawa shaguna a filin Masallacin Idi dake jihar.

Gwamnatin ta Kanoda yan kungiyar masu shaguna sun cimma matsayar haka ne cikin wata yarjejeniya da suka cimma a ranar 12 ga watan Disamba aka kuma gabatar da ita gaban kotu a ranar 13 ga wata.

Lauyoyin bangarorin biyu sun cimma matsayar ne gaban mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya dake Abuja.

A farkon wannan shekarar ne gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da rushe wasu gine-gine da tace sun saba ka’ida yan kwanaki kaɗan bayan rantsar da ita.

More from this stream

Recomended