Mai ba da shawara kan tsaro na kasa, Nuhu Ribadu, ya yi gargadin cewa hana tsaro a karkashin mulkin Shugaba Bola Tinubu ba za a lamunta ba, kamar yadda Hukumar Dillancin Labarai ta Najeriya (NAN) ta ruwaito.
Ya bayyana haka ne a taron Babban Kwamandan Kwastam da aka gudanar a Abuja, ranar Laraba, inda ya jaddada kudirin Shugaban Kasa na kawar da ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da sauran masu barazana ga tsaro.
A cewar Ribadu, dabarun gwamnatin na musamman sun haifar da hallaka daruruwan ‘yan ta’adda a kullum, lamarin da ya tilasta wa da yawa tserewa zuwa kasar Chadi.
“Wannan ya sanya shugaban kasar Chadi ya bayyana yaki da su.
“Za mu samar da tsaro a kasar nan, za mu gyara ta, ba mu da wasa,” in ji shi.
Ribadu ya tabbatar da cewa gwamnati na aiki tukuru don samar da ingantaccen tsaro, wanda ya zama wajibi don ci gaban kasar.