Gwamnatin Tarayya ta yi gargadi game da cin ‘ganda’

Sakamakon barkewar cutar anthrax a wasu kasashe da ke makwabtaka da ƙasar nan, an shawarci ‘yan Najeriya da su daina cin naman daji da ganda.

Ma’aikatar Gona da Raya Karkara ta Tarayya ce ta bayar da wannan gargadi a ranar Litinin a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Dr. Ernest Umakhihe, babban sakataren ma’aikatar.

Umakhihe ya yi nuni da cewa, akwai bukatar a sanar da ‘yan Najeriya game da bullar cutar da ke ci gaba da yin barna a arewacin Ghana, mai iyaka da Burkina Faso da Togo.

Ya bayyana cewa anthrax yana yaduwa daga dabbobi marasa lafiya zuwa mutane tun da cutar ta kasance a cikin ƙasa kuma akai-akai tana cutar da na gida da na daji.

Alamominta sun haɗa da alamun mura kamar tari, zazzaɓi, da ciwon tsoka, kuma idan ba a gano shi ba kuma a yi saurin magance shi, yana iya haifar da ciwon huhu, matsalolin huhu mai tsanani, wahalar numfashi, firgita, har ma da mutuwa.

More News

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...

Mutane 18 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota

Aƙalla fasinjoji 18 ne suka ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Ojebu-Ode zuwa Ore a yankin Ogbere dake...

AMBALIYA: Bafarawa ya ba wa al’ummar Sokoto gudunmawar naira biliyan 1

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya bayar da gudummawar Naira biliyan daya ga al’ummar Sokoto, domin rage radadin wannan annoba.An bayyana hakan...

Ƴanbindiga sun kai hari coci-coci a Kaduna, sun kuma yi garkuwa da mutane

Mutane 3 ne ake fargabar sun mutu, sannan an yi garkuwa da wasu 30 bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a...