
Ma’aikatar aikin gona da raya karkara ta tarayya ta tabbatar da bullar cutar Anthrax a wasu gidajen gona a jihar Niger.
Amma kuma gwamnatin ta gaza bayyana sunayen gonakin da aka samu bullar cutar da kuma kamarin bazuwar ta.
Cutar Anthrax cuta ce nau’in Bacteria dake shafar dabbobi irinsu shanu, akuya tunkiya da sauran su kuma mutane suna iya daukar cutar daga dabbobin.
A wata sanarwa ranar Litinin mai dauke da sa hannun Columba Vakuru, babban jami’in kiwon lafiyar dabbobi na Najeriya ta ce akwai sanarwa da aka samu ranar 14 ga watan Yuli cewa an samu wasu dabbobi dake nuna alamar cutar Anthrax a wani gidan gona mai dauke da dabbobi iri-iri a Suleja dake jihar Niger.
Vakuru ya ce wasu daga cikin dabbobin da suka kamu da cutar sun nuna alamun da suka haɗa da fitar da jini ta dubura, hanci, ido da kuma kunne.