Gwamnatin tarayya ta lalata hauren giwa da aka kwace a Abuja

Gwamnatin tarayya ta lalata hauren giwa mai nauyin tan 2.5 da aka kwace a Abuja.

Jami’an ma’aikatar kula da muhalli ne suka jagoranci bikin lalata hauren giwar a ranar Talata.

Da yake magana a lokacin da ake lalata hauren giwar karamin ministan ma’aikatar muhalli, Ishaq Salako ya ce lalata hauren giwar da aka kwace ya nunawa duniya cewa Najeriya bata amince ba da safarar haramtattun sassan jikin dabbobin daji ba.

Ya kara da cewa hakan zai kuma zama gargadi ga masu amfani da Najeriya a matsayin hanyar safarar haramtattun sassan dabbobin daji.

More from this stream

Recomended