Gwamnatin tarayya ta kwaso yan Najeriya 108 daga Jamhuriyar Nijar

Gwamnatin tarayya ta ce yan Najeriya 108 masu tafiya cirani ƙasashen Turai da suka maƙale a ƙasar Nijar aka dawo da su gida.

A wata sanarwa a shafin X wanda a baya ake kira da Twitter, Alexander Oturu shugaban shiyar kudu maso yamma na hukumar lura da yan gudun hijira da kuma waɗanda suka rabu da muhallinsu ta Najeriya ya ce akwai jarirai cikin waɗanda aka dawo da su.

Oturu ya ce an samu nasarar kwaso mutanen ne da taimakon Hukumar Kula Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya da kuma ofishin jakadancin Najeriya dake Niamey.

Ya ce yan Najeriya da aka dawo da su sun haɗa da maza 32, mata 29 da kuma yara 44 sai kuma jarirai 3.

More from this stream

Recomended