Gwamnatin tarayya ta kaddamar da motoci masu amfani da iskar gas ta CNG

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin shugaban kasa na samar da motoci masu amfani da iskar gas ta CNG.

Shirin an samar da shi ne domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur da gwamnatin ta yi.

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila shi ne ya kaddamar da shirin ranar Juma’a a fadar shugaban kasa.

A ƙarkashin shirin za a samar da cibiyoyi shida a fadin Najeriya da za a riƙa aikin mayar da motoci masu amfani da man fetur ya zuwa iskar gas ta CNG.

More from this stream

Recomended