Wata babbar kotun tarayya a ranar Laraba ta sallami, Bello Bodejo shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore.
An wanke Bodejo daga zargin aikata ta’addanci da gwamnatin tarayya take tuhumarsa da aikatawa.
Inyang Ekwo alƙalin dake sauraron shari’ar shi ne ya sanar da hukuncin bayan da Aderonke Imana lauyan dake wakiltar ofishin Antoni Janar ta shigar da buƙatar janye tuhume-tuhume uku da gwamnatin ta ke yiwa Bodejo.
Lauyar ta gabatar da buƙatar janye ƙarar ne bisa dogaro da sashe na 108 na kundin shari’ar manyan laifuka.
Tawagar lauyoyin Bodejo ba su nuna adawarsu ba ga buƙatar ta gwamnatin tarayya.
A ranar 23 ga watan Janairu ne jami’an tsaro suka kama Bodejo a ofishin Miyetti Allah dake Karu a jihar Nasarawa bayan da ya kaddamar da kungiyar bijilante a jihar.
Bodejo ya ce kungiyar za ta taimakawa jami’an tsaro wajen shawo kan matsalar tsaro a yankin arewa ta tsakiya.