Gwamnatin tarayya ta hana sayar da iskar gas ƙasashen waje

Gwamnatin tarayya ta sanar da hana sayar man iskar gas na LPG da ake girki da shi ya zuwa ƙasashen waje.

Ekperikpe Ekpo ƙaramin ministan harkokin mai ɓangaren iskar gas shi ne ya sanar da haka ranar Alhamis a lokacin wani taron masu ruwa da tsaki.

Ya ce matakin an ɗauke shi ne da gangan domin tabbatar da wadatuwar iskar a kasuwar cikin gida da kuma sauƙaƙawa mutane saboda yadda gas ɗin yayi tsada.

Ya ƙara da cewa tabbas idan aka samu wadatuwar iskar gas ɗin to kuwa babu makawa farashinsa zai yi ƙasa.

” Ina magana da hukumar NMDPRA dake saka ido muna yin taruka kusan kullum da kuma kamfanonin da suke samar da gas irinsu Shell,Mobil da Cheveron akwai fatan cewa abubuwa za su canza. Bama buƙatar muyi ta surutu akan batun.” Ya ce

More from this stream

Recomended