Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranakun Hutun Kirsimeti Da Na Sabuwar Shekara

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin 25 da kuma ranar Talata 26 ga watan Disamba 2023 sai kuma ranar Litinin 1 ga watan Janairun 2024 a matsayin ranakun bikin hutun kirsimeti da na sabuwar shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olabunmi Tunji Ojo shi ne ya bayyana haka a maddin gwamnatin tarayya a cikin wata sanarwa ranar Juma’a mai dauke da sa hannun, Peter Egbodo mai rikon mukamin babban sakatare a ma’aikatar.

Ministan ya taya al’ummar kirista murnar bikin na kirsimeti kana ya shawarce su da su yi koyi da Yesu Kiristi kan halayen da ya aikata da kuma wadanda ya koyar.

Ya kara jaddada cewa tsaro da zaman lafiya su ne ginshikin cigaban tattalin arziki da kuma cigaba.

More from this stream

Recomended