Gwamnatin Najeriya ya bai wa Guinea Bissau gudummawar miliyan 180

0
Muhammadu Buhari

Hakkin mallakar hoto
Nigeria Presidency

Image caption

Shugaba Muhammadu ya bayar da taimakon ne bisa kokon barar da Guinea ta miko masa

Shugaba Muhammadu ya bai wa kasar Guinea Bissau gudummawar dala 500,000, kwatankwacin kusan naira milyan 180 domin gudanar da zabe a kasar.

A wani jerin sakonni da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Garba Shehu ya bayyana cewa kasar ta Guinea ce ta bukaci da Buhari ya tallafa mata.

A ranar 10 ga watan Maris din 2019 aka gudanar da zaben ‘yan majalisa a Guinea Bissau. wanda jam’iyya mai mulkin kasar ta PAIGC ta lashe kujeru mafiya yawa.

Garba Shehu ya ce Buhari ya bayar da taimakon dala 500,000 “bisa tsananin bukata da gwamantin kasar Guinea ta nuna don gudanar da zabukanta”.

Sauran kayayyakin sun hada da akwatunan jefa kuri’a 350, babur guda 10, da kuma motar a-kori-kura guda biyu.

Shugaban ya umarci ministan harkokin kasashen wajen Najeriya Geoffrey Onyeama, da ya yi masa wakilci a kasar ta Guinea.

Onyeama zai wakilci Shugaban ne a matsayinsa na shugaban zauren shugabannin kasashe mambobin kungiyar ECOWAS, kungiyar habaka tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka.

Zai kuma hadu da shugaban kungiyar ta ECOWAS Jean-Claude Brou a babban birnin kasar ta Guinea Bissau.

A wata ziyarar ta daban kuma, ministan zai kai ziyarar aiki Cotonou babban birnin kasar Benin.

Ziyarar ta biyo bayan rikice-rikicen siyasa ne a kasar gabanin zaben ‘yan majalisa da za a gudanar ranar 28 ga watan Afrilu.

Ministan zai gabatar da sakon Shuagaba Buhari na musamman ga Shugaba Patrice Talon na Benin.

A ranar Alhamis Shugaba Buhari ya tafi birnin Landan a wata ziyara ta kashin-kai, kamar yadda fadarsa ta bayyana.

Ziyarar na zuwa ne a lokacin da wasu rahotanni ke cewa Shugaban yana yunkurin yi wa majalisar ministocinsa garambawul a yayin da yake shirin fara wa’adi na biyu a matsayin shugaban kasa ranar 29 ga watan Mayu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here