Gwamnatin tarayya ta gurfanar da Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin Najeriya da aka dakatar,bisa tuhume-tuhume biyu da suka hada da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
An gurfanar da shi ne a gaban babbar kotun tarayya.
A cewar rahoton gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi, gwamnatin tarayya ta zargi Emefiele da mallakar bindiga ba tare da lasisi ba.
Gwamnati ta yi iƙirarin laifin ya ci karo da Sashe na 4 na Dokar Makamai.
Baya ga tuhumar, ana tuhumar Emefiele da mallakar harsashi har guda 123 ba tare da lasisi ba.