Gwamnatin tarayya ta fara biyan albashin malaman jami’o’in da aka riƙe a karkashin kungiyar malaman jami’o’i.
Majiyoyi da dama a bangaren ilimi sun tabbatar wa manema labarai a Abuja sabon lamarin a ranar Litinin.
Shugaban ASUU na Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna, Farfesa Gbolahan Bolarin, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce, “Eh gaskiya ne. An fara biyan kuɗi.”
A watan Oktoban 2023 ne dai shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da sakin albashin hudu daga cikin watanni takwas na ASUU da gwamnati ta hana a baya.