Gwamnatin Najeriya ta ƙara kuɗin yin faso a faɗin ƙasarta

Gwamnatin tarayya ta sanar da karin kudin da ake kashewa wajen karbar fasfo din Najeriya. 

Kakakin Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), DCI Kenneth Udo, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a daren Laraba a Abuja, ya ce matakin wani bangare ne na kokarin tabbatar da ingancin fasfo din Najeriya. 

A cewarsa, sabbin sauye-sauywen za su fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Satumba, 2024.

“Bisa bitar, littafin fasfo mai shafuka 32 tare da aiki na tsawon shekaru 5 wanda a baya aka caje shi akan Naira Dubu Talatin da Biyar (N35,000.00) zai zama naira dubu hamsin (N50,000.00) kacal, yayin da takardar fasfo mai shafi 64 mai inganci na shekara 10, wadda ta kasance Naira Dubu Saba’in (N70,000.00), yanzu za ta zama naira dubu ɗari (N100,000.00) kacal.

“Duk da haka, kudaden ba su canza ba a kasashen waje.

More from this stream

Recomended