Gwamnatin Katsina Ta Fara Sayar Da Hatsi Kan Farashi Mai Sauki

Shirye-shiryen sun yi nisa a ƙoƙarin da gwamnatin jihar Katsina take yi na sayarwa da al’ummar jihar kayan abinci cikin farashi mai sauƙi.

Tuni aka kammala shirin fara rabon hatsi ya zuwa ƙananan hukumomin jihar 34.

A kwanakin baya ne gwamnan jihar, Mallam Dikko Umar Radda ya yi alƙawarin sayar da hatsin kan farashi mai sauƙi a ƙoƙarin ragewa al’umma raɗaɗin matsin tattalin arziki da ake fama da shi.

A cewar gwamnatin jihar kayan abinci  za a sayar sun haɗa da Gero,Masara da kuma Dawa.

Za a riƙa sayar  da kwanon kowanne daga ciki kan kuɗi ₦500 a maimakon farashin ₦1500 da ake sayarwa a kasuwa.

More from this stream

Recomended