Gwamnatin Kano Za Ta Rabawa Ɗaliban Jihar Su 6500 Fom Na Jarrabawar UTME

Gwamnan jihar Kano,Engr Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da shirin raba fom ɗin jarrabawar UTME ga ɗaliban sakandaren jihar dubu 6500.

A wata sanarwa gwamnan ya ce ya yi hakan ne domin samar da damarmaki ga ɗaliban jihar na halartar makarantun da suke gaba da sakandare.

“A ƙoƙarin mu na samar da damarmaki na cigaba da karatun gaba da sakandare ga ƴan asalin jihar Kano na ƙaddamar da rabon fom ɗin jarrabawar JAMB UTME  guda 6500 ga ɗaliban makarantun sakandare,” ya ce.

Ya ce gwamnatinsa ta samu cimma manyan nasarori a bangaren bunƙasa ilimi a jihar a cikin watanni goman da suka gabata da suka haɗa da dawo da shirin tura ƴan asalin jihar ƙaro karatu a jami’o’in ƙasashen waje, biyan kuɗin makaranta na ɗaliban jihar dake manyan makarantu da sake buɗe makarantu 21 na koyon sana’a.

More News

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...

Hukumar NDLEA ta lalata sama da tan 300 na miyagun kwayoyi da aka kama a Legas da Ogun

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta yi nasarar lalata kilogiram 304,436 da lita 40,042 na haramtattun abubuwa da...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...