Gwamnatin jihar Kano ta dawo bayar da tallafin karatu na gaba da digiri na biyu ga ‘yan asalin jihar.
An bayyana hakan ne a ranar Juma’a ta wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Kano, Dakta Abdullahi Baffa Bichi.
Ana kira ga daliban da suka kammala karatun digiri na farko waɗanda suka fito daga jihar kuma suke da ƙoshin lafiya don tafiya ƙasashen waje.
Ya kuma bayyana cewa karo na karshe da jihar ta bayar da irin wannan tallafin shi ne a shekarar 2025, lokacin gwamnatin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.