Jam’iyyar mai jiran gado a Jihar Kano, wato NNPP, ta yi zargin gwamnatin jihar mai barin gado da yin kafar ungulu ga shirin miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayu na wannan shekarar.
A wani taron manema labarai a ranar Juma’a, shugaban kwamitin miƙa mulki na gwamna a jam’iyyar NNPP Dr Abdullahi Baffa Bichi ya yi zargin cewa gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, da gangan tana kawo cikan ga shirin miƙa mulki.
Ya ce gwamnatin ta bai wa jam’iyyar NNPP gurbi uku kawai a cikin kwamitin da aka kafa don miƙa mulki hannun sabuwar gwamnati.
Sai dai gwamnati mai barin gado ta Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta musanta wannan zargi.