A yanzu dai za a iya cewa ruwa tasha bayan da gwamnatin jihar Kano ta wanke, Hon. Alhassan Ado Doguwa daga zargin aika ta kisan kai da ake masa.
A wata sanarwar da ma’aikatar shari’a ta jihar Kano ta fitar ta ce bata da gamsassun hujjojin da za su saka ta tuhumar Doguwa kan zargin aikata kisan kai da kuma tayar da zaune tsaye da ake masa.
Sanarwar ta ce ma’aikatar ta dogara ne da rahoton bincike da hukumar yan sanda ta gabatar mata.