Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin aikin hajjin bana da aka ƙara.
Gwamnan ya sanar da haka ne a yau cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce gwamnan ya ɗauki matakin ne biyo bayan ƙarin kuɗin Aikin Hajji da aka samu a wannan shekarar na naira miliyan ₦1.9.
A yanzu dai maniyatan da suka fito daga jihar ta Kano za su biya cikon miliyan 1.4.