
Yaran da basu gaza 7 ne da suka fito daga Bauchi gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya miƙa su ga iyayensu.
Bayanin haka na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.
Gwamnan ya yaba da kokarin rundunar yan sandan jihar karkashin jagorancin, kwamishina Muhammad Hussaini Gumel.
Yusuf ya bayyana kaduwarsa kan yadda aka sato yaran daga Bauchi kuma a kayi kokarin safarar su zuwa jihohin Lagos da Anambra domin a sayar da su.
Gwamnan ya shawarci iyaye da su kasance masu sanya idanu akan ƴaƴansu kana ya shawarci gwamnatin jihar Bauchi da ta tabbatar an hukunta mutanen da aka kama.
Da yake mayar da martani, Mallam Saad ɗaya daga cikin iyayen yaran mai suna Abdulmutallif ya godewa gwamnatin jihar Kano da kuma rundunar ya sandan jihar Kano.
Gwamnan ya kuma bawa yaran tallafin kudi naira dubu ɗari biyar.