Gwamnatin Kano ta kwato motocin kwashe shara 12 da gwamnatin Ganduje ta sayar

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta samu nasarar kwato wasu motocin dibar shara da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ta sayar da su ba bisa ka’ida ba.

A baya dai lokacin da tsohon gwamnan yake mulki an zarge shi da hada baki da wani kamfani mai zaman kansa ta hanyar kulla yarjejeniyar hadin gwiwa da ta kai ga an mallakawa kamfanin motoci da dama mallakin hukumar kwashe shara ta jihar.

Matocin da aka kwato sun hada tifofi 12 da kuma katafila guda daya.

More from this stream

Recomended