HomeArewaGwamnatin Kano ta fara rusau

Gwamnatin Kano ta fara rusau

Published on

spot_img

A kokarinsa na cika alkawuran yakin neman zaben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin rusa wasu haramtattun gine-gine da aka gina a jihar.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce rusa gine-ginen ba bisa ka’ida ba ya zama dole saboda yana cikin alkawuran yakin neman zaben gwamnan.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa za a rushe gine-ginen da aka gina a makarantu, masallatai, wuraren wasan yara, makabarta, kasuwanni, da asibitoci domin tabbatar da bin ka’idar tsara birane da kawata su.

“Wadannan wuraren ana amfani da su ne don amfanin jama’a, don haka abin takaici ne ganin yadda ’yan kasa marasa kishin kasa ke lalata da kuma sauya wuraren jama’a ba tare da an katse suba.

“Za mu kawo karshen kwacen filaye da gina gine-ginen ba bisa ka’ida ba a jihar,” inji shi.

Latest articles

Ƴansandan Najeriya sun hallaka ƴan fashi a Abuja

Rundunar 'Yan sandan Birnin Tarayya ta kashe wasu ‘yan fashi guda biyu yayin musayar...

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana aniyarsa ta gabatar da buƙatar...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje jihar Borno. Buhari ya kai ziyarar...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar Endbadgovernance sun gana da mataimakin...

More like this