
Kamfanin Stallion Auto Keke Limited ya mika baburan Bajaj masu kafa uku guda 140 ga gwamnatin jihar Yobe.
Ma’aikatar samar da ayyukan yi ce ta jihar ta karbi baburan a karkashin shirin gwamnatin jihar na bunkasa masu kananan da matsaikatan sana’o’i a jihar.
Gwamna Mai Mala Buni wanda ya kaddamar da baburan ya ce wani bangare ne na kokarin gwamnatin sa na bunkasa samar da sana’o’i ga matasa.
Ya ce ” babu tantama kanana da kuma matsaikatan sana’o’i za su iya samar da damarmakin ayyukan yi domin yakar talauci.”