Gwamnatin jihar Katsina ta fara rabon kayan abinci da tallafin ₦5000

Gwamnatin jihar Katsina ta ƙaddamar da shirinta na tallafawa mata masu rauni da kuma dattawa inda za a raba musu kayan abinci ga mutanen 33,000..

A wani bangare na ciyarwar watan Azumin Ramadana gwamnatin jihar ƙarƙashin jagoranci mai girma gwamna,Dikko Umar Raddata fara rabon na buhun  shinkafa mai nauyin 25kg da kuma tallafin kuɗi na ₦5000 ga mata masu rauni da kuma mutane mara sa galihu dake faɗin ƙananan hukumomi 31 dake jihar.

Gwamnatin ta ce ta ƙirƙiro tsarin ne na jin ƙai domin ragewa jama’a wahalhalun da ake fama da su na matsin tattalin arziki da tsadar kayan abinci.

More from this stream

Recomended