Gwamnatin jihar Kaduna, ta kafa wani kwamiti da zai biya diyya tare da tallafi ga mutanen da harin jirgin sama marar matuki na rundunar sojan Najeriya ya kai kan mutanen ƙauyen Tudun Biri dake ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.
A ranar Lahadi ne mutane sama da 100 da suka taru a wurin wani taron Maulidi suka gamu da ajalinsu bayan da wani jirgin sama ya sakar musu bam.
Tuni rundunar sojan ta amsa laifin kai harin da tace an kai shi ne a bisa kuskure lokacin da jirgin ke aiki kai hari kan ƴan ta’ada da su ke a yankin.
A wata sanarwa ranar Talata mataimakiyar gwamnan jihar, Hadiza Balarabe Sabuwa ta sanar da kafa kwamitin lokacin da ta jagoranci tawagar wakilan gwamnati ya zuwa ƙauyen.
Hadiza ta ce kwamitin zai ƙunshi manyan jami’an gwamnati, shugabanni addini da kuma wakilan rundunar sojan Najeriya.