Gwamnatin Bauchi Na Shirin Magance Rikicin Manoma Da Makiyaya

Kwamitin ya ziyarci kananan hukumomi ashirin da suke jihar inda ya duba filayen noma da kuma burtalin shanu da ke kawo rigima tsakanin manoma da kuma makiyaya.

Shugaban kwamitin Surveyor Yahaya Baba, ya ce dukkanin manoma da kuma makiyaya su na sana’ar noma da kiwo saboda abu ne da suka gani a zahiri, akan haka ya bukaci ganin manyan filayen noma da wassu ke mallaka an rabawa jama’a.

Yahaya Baba, ya kara da cewa kwamitin ya baiwa gwamnati shawara cewa, duba da yawan jama’a a wannan lokaci, yakamata a rage girman manyan gonaki saboda a ba wasu kuma dama.

Gwamnan Bauchi Bala Abdulkadir Muhammed, ya ce gwamnatinsa tana da kudurin yin gyara, “sabili da haka a duk lokacin da aka buga gangar gaskiya toh ya zama dole ta taka rawa.”

Ya ci gaba da cewa muddin ba a samu maslaha ko gyara a wannan abin da ake yi ba, gaskiya ba za a samu zaman lafiya ba.

Wani mamban kwamitin, Alhaji Muhammadu Sanusi, kuma shugaban kungiyar Fulani ta Kautal Hore a jihar Bauchi, ya yaba da aikin kwamitin da kuma hangen nesan gwamnan jihar Bauchin na kafa kwamitin.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...