Gwamnan Kogi ya ba da umurnin rufe asusun jiha da na kananan hukumomi

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayar da umarnin rufe asusun ajiyar kananan hukumomi da na jihar nan take.

Wata sanarwa da kwamishinan kudi, Asiwaju Asiru Idris ya fitar ta tabbatar da hakan.

Sanarwar ta ce: “Ba za a yi wa kowa wani abu ko wani nau’i na biyan kudi daga Asusun Gwamnati ba.

“An soke umarnin tsayawa da kuma umarnin saka hannun jari nan da nan.”

Ya zuwa yanzu Arewa.ng ba ta samu wata sanarwa da ta bayyana dalilin daukar wannan mataki ba.

More from this stream

Recomended