Gwamnan Kebbi ya raba motocin alfarma ga sarakunan jihar

Gwamnan jihar Kebbi, Nasiru Idris ya miƙa kyautar mota ƙirar Toyota Land Cruiser ga sarakuna huɗu na  jihar masu daraja ta ɗaya.

An miƙa muƙullan motocin ɗaya bayan ɗaya  ga sarakunan da suka haɗa da Sarkin Gwandu Alhaji Muhammad Iliyasu Bashar, Sarkin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammadu Mera, Sarkin Yauri Dr Muhammad Zayyanu Abdullahi da kuma wakilin Sarkin Zuru, Janaral Muhammad Sani Sami.

Gwamnan ya ce ya bayar da kyautar motocin ne saboda muhimmancin da  gwamnatinsa  take bawa dukkanin bangarorin gwamnati.

Ya ƙara da cewa suna sane da irin rawar da sarakunan suke takawa wajen wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

More from this stream

Recomended