Gwamnan Kebbi ya bawa kauyen da bindiga suka kai hari tallafin naira miliyan 7

Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya bada gudummawar naira miliyan N7 ga mutanen ƙauyen Kanzanna a gundumar Tilli dake ƙaramar hukumar Bunza domin rage raɗaɗin harin yan bindiga a yankin.

Idris ya sanar da bada tallafin ne a yayin ziyarar ta’aziyya garin bayan da harin yan bindiga suka kai inda suka kashe mutane uku.

Gwamnan ya jaddada aniyarsa gwamnatinsa na kare rayuka dukiyar al’umma.

“Mun zo ne mu miĆ™a saĆ™on ta’aziyyarmu kan abinda ya faru. Muna rokon Allah ya jikan waÉ—anda suka rasa rayukansu a harin ya kuma bawa iyalansu hakurin jure rashin da suka yi” a cewar gwamnan.

A yayin ziyarar gwamnan na tare da jami’an tsaro na hukumar DSS, sojoji, yan sanda,Civil Defence da kuma yan bijilante.

Ya kuma yin alkawarin bawa jami’an tsaro duk gudunmawar da suke bukata domin samar da tsaro a jihar.

More News

Lauya ya nemi kotu ta bashi mako 4 ya nemo inda Yahaya Bello ya É“uya

Abdulwahab Mohammed babban lauyan tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya nemi babbar kotun tarayya dake Abuja da ta bashi makonni huÉ—u domin ya...

ĆŠalibai 9 aka tabbatar da yin garkuwa da su daga jami’an jihar Kogi

Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da cewa É—alibai 9 aka tabbatar sun É“ace bayan da wasu Ć´an bindiga suka kai farmaki Jami'ar Kimiya da...

Mayaƙan Boko Haram Biyu Sun Miƙa Kansu Ga Sojoji

Aƙalla mayaƙan Boko Haram biyu ne suka miƙa kansu ga dakarun sojan Najeriya na rundunar Operation Haɗin Kai a yankin gabashin jihar Borno. Mayaƙan biyu...

Isa Dogonyaro ĆŠan Majalisar Tarayya Daga Jihar Jigawa Ya Rasu

Isa Dogonyaro wakilin al'ummar ƙananan hukumomin Garki da Baɓura a majalisar wakilai ta tarayya ya rasu. Ɗaya daga cikin abokan aikin marigayin a majalisar tarayya,...