Gwamnan Katsina ya sauke wani kwamishina daga mukaminsa

Gwamnan jihar Katsina, Malam Umar Dikko Radda ya sauke kwamishinan wasanni, Hon. Abdu Abu Dan Kum.

Umar Dikko ya kuma ba da umarnin sake fasalin gudanarwar Katsina United nan take.

“Gwamnan jihar Katsina Malam Umar Dikko Radda ya kori kwamishinan matasa da wasanni. An ba da umarnin sake fasalin gudanarwar Katsina United nan take,” wani dan jaridan wasanni da ke zaune a jihar Katsina ya bayyana wa ƴan jarida.

More from this stream

Recomended