Gwamnan Kano ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautun jihar

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautun jihar ya kuma sanar da sake naÉ—a, Muhammad Sanusi a matsayin Sarkin Kano.

Yusuf ya bayyana haka ne jim kaÉ—an bayan da ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautu ta jihar da majalisar dokokin jihar ta yiwa garambawul.

Gwamnan ya saka hannu ne akan dokar da misalin Æ™arfe biyar 05:10 a gidan gwamnatin jihar a yayin wani Æ™warya-Æ™waryan taro da ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da kuma shugaban majalisar dokokin jihar.

A shekarar 2020 tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya sauke Sanusi daga Sarkin Kano kana ya ƙirƙiro ƙarin wasu masarautu guda biyar.

Har ila yau gwamnan ya bawa sarakunan sauran masarautu huÉ—u da sabuwa dokar ta soke da su sauka daga muÆ™aminsu cikin sa’o’i 48.

More News

Shan giya na halaka sama da mutum miliyan 2.6 duk shekara—WHO

Wani rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ya nuna cewar shan giya na kashe mutum miliyan 2.6 a duk shekara. Rahoton ya ƙara da cewa...

Ƴan fashin daji sun kashe ƴan bijilante 4 da ɗan sanda ɗaya a Kaduna

Wasu da ake zargin ƴan fashin daji ne sun kai farmaki mazaɓar Kakangi dake ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna inda suka kashe...

Ƴan Boko Haram sun yi garkuwa da wani alƙali da matarsa a jihar Borno

Mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun yi garkuwa da alƙalin babbar kotu mai Shari'a, Haruna Mshelia tare da matarsa da kuma dogarinsa. Rahotanni sun bayyana cewa...

Abdul Aziz Yari ya dauki nauyin karatun dalibai 1,700 a Jihar Zamfara

Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta yamma, Abdulaziz Yari Abubakar, ya baiwa 'yan asalin jihar 1,700 tallafin karatu a...