Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautun jihar ya kuma sanar da sake naɗa, Muhammad Sanusi a matsayin Sarkin Kano.
Yusuf ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan da ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautu ta jihar da majalisar dokokin jihar ta yiwa garambawul.
Gwamnan ya saka hannu ne akan dokar da misalin ƙarfe biyar 05:10 a gidan gwamnatin jihar a yayin wani ƙwarya-ƙwaryan taro da ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da kuma shugaban majalisar dokokin jihar.
A shekarar 2020 tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya sauke Sanusi daga Sarkin Kano kana ya ƙirƙiro ƙarin wasu masarautu guda biyar.
Har ila yau gwamnan ya bawa sarakunan sauran masarautu huɗu da sabuwa dokar ta soke da su sauka daga muƙaminsu cikin sa’o’i 48.