Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gana da mai bawa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu.
Ganawar ta gudana ne a ofishin Ribadu dake Abuja.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a Facebook gwamnan ya ce ganawar tasu tayi armashi sosai.
Ziyarar ta gwamnan Yusuf na zuwa ne dai-dai lokacin da ake cigaba da dambarwa kan batun sarautar Sarkin Kano tun bayan sanya hannu kan sabuwar dokar masarautu ta jihar da majalisar dokokin jihar ta yi wa gyara.
Aiwatar da dokar ya sa aka tube Sarkin Kano Aminu Ado Bayero inda aka maye gurbinsa da tsohon sarki Muhammadu Sanusi II.
A makon da ya gabata ne mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdul Salam ya yi zargin cewa Ribadu na da hannu dumu-dumu a rikicin sarautar zargin da Ribadu ya musalta kuma ya yi barazanar shigar da ƙara gaban kotu matuƙar mataimakin gwamnan bai fito fili ya bashi haƙuri ba.
A yayin wani taron manema labarai mataimakin gwamnan ya bawa Ribadu haƙuri.