Gwamnan Kano ya bawa ƴan kasuwar Kantin Kwari da gobara ta shafa tallafin miliyan ₦100

Gwamnan jihar Kano,Abba Kabir Yusuf ya sanar da bada tallafin kuɗi miliyan ₦100 a madadin gwamnatin Kano ga mutanen da iftila’in gobara ya faɗawa a kasuwar Kantin Kwari dake jihar.

Gwamnan ya sanar da bayar da tallafin ne lokacin da ya jagoranci wata tawagar manyan jami’an gwamnati zuwa ziyarar jaje a kasuwar ranar Alhamis.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ya ce   gwamna, Abba Yusuf   ya miƙa saƙon jajen gwamnatin Kano ga ƴan kasuwar da kantunansu suka ƙone a gobarar..

Gwamnan ya ce tallafin kuɗin ba zai zama diya ba na abun da suka rasa a gobarar face an yi ne domin rage musu raɗaɗin asarar da suka yi.

Tun da farko a jawabinsa shugaban hukumar kasuwar Kantin Kwari, Alhaji Hamisu Sa’adu Dogon Nama ya ce shaguna 29 suka ƙone a kasuwar inda ya ya bawa jami’an hukumar kashe gobara kan ɗaukin gaggawa da suka kai kasuwar.

More from this stream

Recomended