Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da murabus ɗin Injiniya Muhammad Diggol, Kwamishinan Ma’aikatar Kulawa da Ayyuka da Bibiya. Wannan murabus ya fara aiki nan take.
Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin mai magana da yawun gwamnan, Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa, a wata takardar da aka fitar ranar Lahadi.
An nada Injiniya Diggol ne a matsayin Kwamishinan Sashen Sufuri a farkon wa’adin mulkin Gwamna Yusuf a shekarar 2023. Daga baya, an tura shi Ma’aikatar Kulawa da Ayyuka da Bibiya, inda ya yi aiki har zuwa lokacin da ya yi murabus.
Gwamna Yusuf ya nuna gamsuwarsa da jajircewa da sadaukarwar Injiniya Diggol yayin da yake cikin majalisar zartarwa ta jihar. Haka kuma, ya yi masa fatan alheri a rayuwarsa ta gaba.
Fadar Gwamnatin ta jinjina wa Injiniya Diggol bisa kishinsa da gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban jihar.