Gwamnan Kano Abba Kabir ya fara rabon kayan tallafi

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya fara rabon buhunan shinkafa ga mazauna jihar.

Ya kara da cewa kimanin mutane 1060 ne za su amfana da wannan, inda ya jaddada cewa za a raba sauran kayan abinci kamar gero, masara da sauransu ga marasa galihu.

Gwamna Yusuf ya ci gaba da cewa gwamnati ta yi wani shiri da ya dace ta hanyar kafa kwamitoci daban-daban domin tabbatar da rarraba kayan abinci yadda ya kamata.

Ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da shirin bada tallafin noma da aka gudanar a Kano.

A cewar sa, matakin na da nufin rage tasirin cire tallafin man fetur.

Ya yi gargadin cewa duk wani jami’in gwamnati da aka samu yana son rai a aikin rabon kayan abinci, za a yi maganinsa yadda ya kamata.

Gwamnan ya ci gaba da bayanin cewa, za a baiwa nakasassu kulawa ta musamman a yayin da ake gudanar da aikin raba kayan agajin, da nufin tabbatar da cewa kayan abinci sun isa ga masu rauni a cikin al’umma.

More News

Gwamnatin Abia za ta fara biyan albashi mafi maranci na naira 70,000 a watan Oktoba

Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da cewa za ta fara biyan sabon albashi mafi karanci na naira 70,000 ga ma’aikatanta daga watan Oktoba 2024.Kwamishinan...

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 32 a yankin Neja Delta

Dakarun sojan Najeriya na runduna ta 6 dake Fatakwal sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 32 tare da ƙwace lita 250,000 na...

An gudanar da bikin cikar Kwankwaso shekara 68.

Tarin magoya baya da kuma abokanan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ne suka halarci taron lakca da aka shirya domin bikin...

Faruk Lawan ya kammala zaman gidan yarin Kuje

An sako tsohon É—an majalisar wakilai ta tarayya, Hon Faruk Lawan daga gidan yarin Kuje bayan da ya kammala zaman gidan yarin na shekaru...