Gwamnan jihar Kano ya ware N700m don biya wa yan asalin Kano a BUK kuɗin makaranta

A wani yunkuri na rage wa dalibai da iyalai matsalolin kudi da suke fama da su a halin yanzu, Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya bayyana kudirinsa ba da tallafin kudi don biya wa ɗaliban jihar Kano kudin makaranta.

Ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook jiya.

Mai taimaka wa gwamnan ya bayyana matakin da majalisar zartarwar jihar Kano karkashin jagorancinsa ta yanke na ware kusan Naira miliyan 700 domin biyan kudin makaranta ga dalibai kusan 7,000 da suka fito daga jihar Kano wadanda suke karatu a Jami’ar Bayero Kano (BUK).

Ana sa ran matakin zai ba da taimako mai mahimmanci na kuɗi ga iyalai waɗanda ke fafutukar biyan kuɗin makaranta a waɗannan lokuta masu tsananin.

More from this stream

Recomended