Gwamnan Jigawa zai biya wa asalin ƴan jihar kuɗin makaranta

Gwamna Umar Namadi ya amince da biyan kudin rijistar ɗaliban Jhar Jigawa wadanda suke karatun digiri daban-daban a Jami’ar Tarayya, Dutse FUD, Jami’ar Bayero, Kano (BUK), Jami’ar Fasaha ta Jihar Kano (KUST) da Jami’ar Maiduguri.

Kuɗin da aka ware ya kai dadin naira miliyan ɗari da sittin da bakwai da dubu ashirin da hudu da ɗari tara da hamsin (N167,024,950.00).

Matakin Majalisar Zartarwar Jihar ya yi dai-dai da tsarin gudanarwa na yanzu don taimaka wa iyaye masu karamin karfi su shawo kan karuwar kudaden makaranta ga ‘ya’yansu.

Hakazalika majalisar ta amince da sake duba tallafin karatu ga ‘yan asalin jihar Jigawa nan take kuma lokacin da za a biya kudaden ya kasance a farkon kowace shekarar makaranta.

More from this stream

Recomended